11 Yuli 2021 - 12:52
​Amurka Ta Bukaci A Warware Takaddama A Kan Madatsar Ruwa Ta Renaissance AU

Gwamnatin kasar Amurka ta bukaci a gaggauta farfado da tattaunawa tsakanin kasashe uku wadanda suke takaddama kan madatsar ruwa ta Renaissance ta kasar Habasha, karkashin jagorancin tarayyar Afrika da kungiyoyun yankin.

ABNA24 : Jaridar Sudan Tribune ta kasar Sudan ta nakalto Linda Thomas-Greenfield jakadiyar Amurka a MDD ta na fadar haka a wata zama a kwamitin tsaro na MDD.

Greenfield ta bukaci a farfado da tattaunawar da gaggawa bisa tsarin da kasashen uku suka rattabawa hannu kuma suka amince da shi a shekara 2015 da kuma ka’idojin da tarayyar Afirka ta gabatar a shekara ta 2020.

Kafin haka dai kasashen Masar da Sudan sun bukaci MDD ta shiga cikin lamarin don warware sabanin da ke tsakanin kasashen uku wadanda kogin nilu ta ratsa cikinsu.

342/